<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ran da aikinmu ya ƙare cikin wannan duniya,
 Za mu hau mu zauna gun Mai Cetonmu,
 Za mu huta daga ƙuncinmu, mu yi ta zamanmu
 Wurin Yesu Kristi, Ubangijinmu.

[V2]
 KORUS
 Za ya kira mu a Sama,
 Za mu shiga gaban Allah,
 Za mu wurin Mai Cetonmu,
 Zuwa gidan da ya shirya dominmu.

[V3]
 2) Can a gida mai darajan nan, a gaban Allahnmu,
 Za mu yi sujada gaban kursiyinsa,
 Za mu haƙa kai da Masu Bi na dukan zamanai,
 Za mu yi ta yabon Yesu, Mai Ceto.
 Korus

[V4]
 3) Can mā gane duk dalilin ƙuncinmu a duniya,
 Za mu gane yawan ceton da ya yi.
 Za mu yi ta yin godiya domin dukan aikinsa,
 Za mu yabi sunan Yesu, Mai Ceto.
 Korus</lyrics>
<title>Ran da Aikinmu Ya Ƙare Cikin Wannan Duniya LW321</title>
<hymn_number>321</hymn_number>
<author>Black, James Milton (1856-1938)</author>
</song>